Bishop na Katolika na yankin Sakkwato, Matthew Kukah, ya shaida wa Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka cewa Gwamnatin Buhari ba ta iya yin komi game da matsalolin tsaro, wanda ta yi alkawarin magancewa kafin ta karbi mulki a 2015.
Ya fadi hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi game da yadda kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a Arewa ke muzgunawa Kiristoci a Najeriya, ga Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Tom Lantos da ke Washington, DC, a Amurka.
Bishop Kukah ya ce har yanzu mutane ba su ga wani kwakkwaran yunkuri na magance rashin tsaro ba, wanda a cewarsa, yana da nasaba da addini da kabilanci.
Kukah wanda Sakataren Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa da kasa ne ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da sanya ‘yan kabilarsa da addininsa a manyan mukaman siyasa da gangan.
“Yankin Arewa, kai har ma da kasar baki daya, yan bindiga da masu satar mutane da sauransu, sun mamaye yankin da kasar. “Lura da gwamnati kamar dai ba da gaske take yi ba ko kuma ba ta da sha’awar kawo karshen lamarin wa?annan mutanen yana kara rikita lamarin.
“Sabanin a nan shi ne cewa Shugaban kasa ya zabi fifita manufofi na siyasa ga wadanda yake addini da kabila iri daya da su.” A cikin shaidar da ya gabatar a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Amurkar, mai rajin kare hakkin dan Adam din ya yi ikirarin cewa rikicin addini da ake yi kan Kiristoci a Najeriya ya kasance yana ta faruwa cikin tsawon shekaru, amma sannu a hankali yawan hare-haren ya karu a cikin shekara 10 da suka gabata.
A cewar Bishop din, masu tsattsauran ra’ayin sun fi maida hankali ne kan makarantun Kiristoci na Arewa, suna cusawa yara tunaninsu tare da maida ‘yan matan zuwa matan aure da masu musu girki da leken asiri kwarkwarorinsu da dai sauransu.
