Bauchi: Za Mu Biya Albashi Kafin Babbar Sallah – Gwamna Bala

A daidai lokacin da Musulmin duniya ke shirye shiryen bikin Babban Sallah, Gwamnatin Jihar Bauchi tasha al’washin ma’aikata zasu yi Sallar cikin walwala da jindadi, don zasu Sami al’bashinsu na wan nan watan Yulin da muke ciki don farantawa iyalansu rai da samun sukunin, sayan dabbobin layya.

Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya sanar da haka a cikin Karamar hukumar Darazo lokacin da yake bada kayan tallafi da suka kai kimanin naira miliyan saba’in, da biyar N75m ga al’ummar yankin karamar hukumar Darazo da kewaye.

Gwamnan yace batun albashi Yana da matukar muhimmanci in akayi la’akari da yanayin jiha ce ta ma’aikata ga Kuma bikin Sallah Babba Yana karatowa kuma yazo a lokacin da wata bai kare ba, don mu faranta ma al’umma jihar, shiyasa muka daukin matakin baiyan albashi in Allah ya yarda kafin cikin satin nan, zasu fara jin al’bashinsu.

Wasu ma’aikatan da muka tattauna dasu sun shaida ma Muryar Yanci’ cewa hakan zai taimaka matuka gaya don gudanar da shagulgulan bikin Sallar, kana suka ce hakan zai kawo saukin tafiyar da al’amurra a yayin bukukuwan Babban Sallar.

To saidai duk da wan nan al’washin na Biyan albashin wadansu sunce, dole ne ma’aikata suyi karatun ta natsu su kashe kadan Kar su rushe albashin kaf wajen sayan naman layya, domin za a dauki lokaci mai tsawo kafi a sake samun albashi, kamar yadda yake faruwa a wasu lokotan da dama a baya

Daga karshe kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da Baburan hawa, injinan markane, kayan Madara da Kuma injinan hada gurguru ga masu kana nan sana’oi da kuma motoci dumbin kudade, da wadanda aka basu naira dubu Hamsin N50, to000 dubu dari 100,000 dama masu dubu dari da Hamsin N150,000 dukkanin su an basu be da zimman rage radadin talauci a fadin Jihar ta fannin bunkasa kasuwanci da kana nan masana’antu a cikin al’umma

Related posts

Leave a Comment