Bauchi: Ambaliyar Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane Da Dabbobi A Ningi

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bukaci gwamnatin tarayya data kawo masa dauki don magance Ambaliyar ruwa da yayi sana diyyar bangarewar babban hanya na gwamnatin tarayya da ya hada Bauchi-Ningi-Jigawa da Kuma Jihar Kano tare da mutuwan mutane Uku da Akuyoyi su dari biyu da Hamsin 250 a Karamar hukumar Ningi, biyo bayan tabka ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren Jumma’a da ta shige a yankin.

Gwamnan yayi rokon ne bayan ziyarar gani da Ido da yakai a ranar Asabar, inda Hanyar ta zabtare gaba daya, da kuma jajantama mutanen yankin irin barnar da ambaliyar ta haifar da kuma asarar rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Ambaliyar dai ta faru ne kadan bayan an wuce kasuwar Gadar Maiwa kafin a karisa shalkwatar karamar hukumar Ningi a ranar Alhamis da daddare.

Rahotanni dai sunyi nuni da cewa an tafka ruwan sama ne kaman bazai taba tsayawa ba kuma ga karfin gaske,Kinsan babban asara ce, don haka ya roki gwamnatin tarayya da tayi wani abu chikin gaggawa don kar mutane su shiga halin ni yasu a yankin, dama matafiya daga sassan kasan nan.

Yace, domin a halin yanzu hada-hada a kan hanyar sun tsaya chak, shiyasa a cewar Gwamnan ya bada izinin masu gyran hanyar da so iso wajen don gyaran inda ya yanke a sana idiyyar ruwan saman.

Bala yace akalla gyran wuraren da ambaliyar ruwa ya lalata a duk fadin Jihar baki daya zai lakume biliyoyin nairori, tare da gina magudanar ruwa da za’ ayi don kaucewa aukuwar ambaliyan ruwan nan gaba

Suma mutanen yankin a halin yanzu saidai su taka da kafansu zuwa dayabangaren kokuma su nemi Baburan na waucin gadi dominna hate dasu kuma hakan ya jefasu ciki kuncin rayuwa, tunda sai sun biya kudade Mai yawa kafin dannmashi ya yarda ya dauke su, shima cikin kasada ne da hatsari suke yin hakan.

Daga karshe Gwamna Bala ya roki mutanen yankin da su kwantar da hankalinsu suyi hakuri tare da tawakkali kan wan nan Ibtila’i a cewarsa komai mutum ya sa mu ko ya rasa duka daga Allah ne

Related posts

Leave a Comment