Da Dumi-Dumi: Kogi Ya Hadiye Dandazon Mayakan ISWAP

Rahotanni daga maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar a?alla maya?an ISWAP 25 ne ruwa ya ci su a cikin kogi yayin da rundunar sojin Najeriya ke fatattakar su a yankin Marte da Tafkin Chadi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta bayyana cewa jiragen ya?in Najeriya ciki har da Super Tucano na sojin saman ?asar sun kai samame a sansanonin ?ungiyar ISWAP a ranakun Laraba da Alhamis.

Wani mazaunin yankin da aka kai samamen ya shaida cewa jiragen saman sun saki bama-bamai a gidajen ajiye makamai na ?ungiyar ta ISWAP.

Wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa jiragen ya?in sun tarwatsa gidajen ajiyan kayayyaki a Bukar Mairam da Jubularam da Abbaganaram da Chikul Gudu.

Sai dai maya?an da suka tsira daga farmakin da aka kai musu a Bukar Mairam da Jubularam sun gudu inda suka yi ?o?arin tsallaka wani kogi da ke yankin tafkin Chadi inda a lokacin ne har 25 daga cikinsu suka nutse a ruwa.

Related posts

Leave a Comment