APC Ta Aike Wa INEC Shirinta Na Gudanar Da Zaben Shugabanni

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar Jam’iyya mai mulki ta APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu domin za?en shugabanni.

Kamar yadda wasikar ta kunsa mai taken “Sanarwa kan gangamin zaben jam’iyya na kasa” kuma shugaban kwamitin, Mai Mala Buni da sakataren kwamiti John Akpanudoedehe suka saka hannu, sun sanar da hukumar zaben hukuncin da suka yanke a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Hatimin da aka buga a wasikar ya bayyana cewa hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ta samu wasikar a ranar 3 ga watan Fabrairun 2022.

“Muna sanar da hukumar cewa jam’iyyar mu ta shirya yin gangamin zaben shugabannin jam’iyyar na kasa ranar 26 ga watan Fabrairun 2022. “Wannan na bayyana sanarwar mu kamar yadda sashi na 85 na dokokin zaben gyararru na 2010 suka tanada.

“Muna bukatar ku shirya jami’an ku domin su lura da zaben yadda ya dace. A yayin da muke fatan samun hadin kan ku, muna tabbatar muku da tsananin girman ku da muke gani,”

Related posts

Leave a Comment