2023: Kungiyoyin Arewa Sun Amince Da Takarar David Umahi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Kimanin Kungiyoyi goma sha tara ne wanda suka fito daga yankin arewacin Najeriya suka amince da takarar Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi a matsayin Shugaban kasa a zaben gamagari dake karatowa na shekarar 2023.

Kungiyoyi wadan da suka dunkule su goma sha tara suka chure wuri guda da ake masu lakabi da Yan’rajin Shugabanci na Gari a Arewa, (AAGG) sunyi wan nan furucin ne a wajen wani taro da suka gudanar a cikin Jihar Bauchi.

Kungiyoyin Matasan dai sunce su a halinda Najeriya take ciki tana bukatan zakakuri Kuma jajirtace kaman David Umahi, sa’annan suka ce suna da yakinin shine dantakara tilo da yayi fice ta wajen salon iya mulki gashi kuma yana da basira da fikira irin na shugabanci.

Alhaji Jamilo Mato shine Shugaban dunkulalliyar Kungiyar matasan arewan, yace baza suyi nadama ba ko kadan don amincewa da wan nan dan’takara a daidai lokacin da zabubbukan gama gari ke kara matsowa

Yace David Umahi shine yayi amfani iliminsa da kwarewarsa wajen zakulo ayyukan da suka chanza labari a Jihar sa ta Ebonyi, cewa in yan’Najeriya suka bashi dama to za suga chanjin da ba’ataba ganin ba na ci gaban kasa baki daya.

Kana shugaban ya kara da cewa Gwamnan Ebonyi zai shimfida ayyukan da kowani dan Najeriya zaiyi alfahari da irin salon shugabancin sa, Kama daga kiwon lafiya, samarda aikin yi ga matasan Najeriya, da Kuma kawar da yunwa a tsakanin al’umma, kana da tsaron rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Daga karshe suka ce zai bunksa tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar marasa galihu abubuwan da zai sa a gaban sa, kana kungiyoyin sun sha alwashin taimaka masa ganin ya zama Shugaban kasa a 2023. Kana sun roki daukacin yan’Najeriya su goyi bayan takarar David Umahi na Ebonyi karkashin Jam’iyyar APC mai mulki don ceto kasar daga matsalolin da ake fama dasu a halin yanzu.

Related posts

Leave a Comment