Hukumar gasar Olympics da ke gudana a Japan ta dakatar da ‘yar tseren Najeriya, Blessing Okagbare, daga gasar saboda ba ta tsallake gwajin shan ?wayoyi masu ?ara kuzari ba.
A ranar Juma’a ne Okagbare mai shekara 32 wadda ta ?ware a tsere da kuma tsalle, ta lashe tseren mita 100 sannan ta samu gurbin shiga zagayen kusa da na ?arshe da za a yi ranar Asabar.
Sashen kula da halayen ‘yan wasa na Athletics Integrity Unit (AIU) ya ce an gano ‘yar tseren ta sha ?wayar da ke ?ara wa wasu ?wayoyin halittar ?an Adam ?arfi biyo bayan wani gwaji da aka yi mata tun ranar 19 ga watan Yuli.
AIU ya ce an sanar da Okagbare game da dakatarwar a ranar Asabar.
‘Yar wasan wadda ta lashe kyautar azurfa (silver) a birnin Beijing a 2008, ta yi nasara a tseren mita 100 cikin da?i?a 11.05, an tsara za ta kara da Asher-Smith da kuma ‘yar Jamaica mai suna Elaine Thompson-Herath a wasan kusa da na ?arshe.
Dakatarwar tata na zuwa ne kwana biyu bayan an hana ‘yan wasan Najeriya 10 shiga gasar bisa dalilin rashin cancanta.
AIU ya ce ba za su shiga gasar ba saboda sun ?i shiga a yi musu gwajin ?wayoyin ?ara kuzari da ake yi kafin fara gasar ta Olympics.
