Mazauna unguwar Malali sun wayi garin Lahadi cikin ?araguzan rukunin gidaje da ke Malali Low-Cost sakamakon rusau da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi.
Bayanan da muka tattara sun nuna cewa da misalin ?arfe 11:30 na daren Asabar ne jami’an tsaro suka isa unguwar da ke ?waryar birnin Kaduna, inda suka fara rushe gine-ginen.
Wani mazaunin unguwar mai suna Titus Katuka ya ce tun shekarar 1976 suke haya a gidajen wa?anda mallakar gwamnatin jihar ne amma a 2017 gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce za ta sayar musu da su.
Ya ce lokaci guda kuma gwamnatin ta ce za ta rushe su domin gina kasuwa a wurin bayan ta mayar wa da wa?anda suka fara biya ku?a?ensu, abin da ya sa suka kai ?ara kotu.
“Ni ba a zo kan layinmu ba amma ban sani ba gobe ko jibi za su iya ?arasowa,” in ji shi.
An gina rukunin gidajen na Malali Low-Cost ne domin masu ?aramin ?arfi.
Rushe-rushen na daren jiya Asabar sun shafi rukunin gidaje ne da ke kan layukan Gambia da Siera Leon na unguwar.
Kazalika mutanen sun ce jami’an tsaro sun harba musu haya?i mai sa hawaye kafin fara aikin rusau ?in.
Wasu hotuna da aka ya?a a shafukan sada zumunta sun nuna ?araguzan gidajen da aka rusa.
A ‘yan shekarun nan gwamnatin Kaduna ?ar?ashin jagorancin Nasir El-Rufai na rusa wurare da ta ce an gina su ba bisa ?a’ida ba, ciki har daa kasuwanni.
