Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 418 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum 113, FCT-86, Abia-47, Kaduna-39,, Rivers-27, Katsina-22, Benue-14, Oyo-13, Kano-12, Enugu-8, Edo-7, Imo-7, Bauchi-6, Ebonyi-6, Ogun-6, Ondo-4 da Nasarawa-1
Yanzu mutum 73,175 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 66,090 sun warke, 1,197 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,888 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,952, FCT 8,424, Oyo 3,760, Edo 2,737, Delta 1,829, Rivers 3,151, Kano 1,904, Ogun2,328, Kaduna 3,867, Katsina -1,197, Ondo 1,751, Borno 758, Gombe 1,069, Bauchi 808, Ebonyi 1,061, Filato 3,997, Enugu 1,363, Abia 973, Imo 688, Jigawa 340, Kwara 1,226, Bayelsa 469, Nasarawa 562, Osun 965, Sokoto 192, Niger 298, Akwa Ibom 364, Benue 501, Adamawa 329, Anambra 290, Kebbi 93, Zamfara 79, Yobe 108, Ekiti 395, Taraba- 196, Kogi 5, da Cross Rivers 90.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa Kashi 10 bisa 100 na wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya ?an kasa da shekara 19 ne.
Ehanire ya kuma ce kimiyya ya nuna cewa tsofaffi musamman wadanda ke da shekaru sama da 60 sun fi kamuwa da cutar da wuri.
Ya ce wadannan mutane na daga cikin rukunin mutanen dake dauke da cutar ba tare da sun nuna alamun cutar ba wanda hakan ya sa za su iya yada cutar ba tare da sun sani ba.
Ministan ya yi kira ga masu makarantu da iyaye da su zage damtse wajen kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare yayan su a lokacin da za a bude makarantu.
