Farashin Mai: Buhari Ya Fahimci Hali Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce shirin da Gwamnatin Tarayya za ta yi na sauya motocin yan Najeriya su yi amfani da Manfetur Gas za su fara da motocin kasuwanci. Ya ce tuni aka fara shirin a jihar Edo inda ya ce kamfanin Dangote ya sauya manyan motoci 4,000 don yin amfani da gas. A cewar wata sanarwa a ranar Litinin ta hannun babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da…

Read More

Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar Da Gandun Kiwon Jakuna

Cibiyar bincike don bunkasa kiwon dabbobi a Najeriya NAPRI da hadin gwiwar wasu abokan hulda za su yi aiki tare domin samar da gandun kiwon jakuna a jihohin Bauchi da Ebonyi. Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya ruwaito shugaban cibiyar Farfesa Abdullahi Mohammed na cewa sun kulla wata yarjejeniya da abokan huldarsu a watan Fabrairu domin samar da jakai miliyan biyu a Najeriya nan da shekara biyar zuwa 10. Farfesan ya ce shirin zai iya samarwa da kasar kudin shiga da suka kai dala biliyan biyu a ko wacce…

Read More

Saudiyya Ta Fi Mu Arziki Da ?arancin Jama’a Shi Yasa Albashin Su Ya Fi Namu – Lai

Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya kare shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan hada Najeriya da kasar Saudiyya da yayi akan farashin Man fetur. A jawabinsa na ranar ‘yanci shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai kamata ace Najeriya na sayar da mai a arha fiyr da kasar Saudiyya ba. Wannan magana ta jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta dana zahiri. Saidai a karewar da yawa shugaban kasar, Lai Muhammad ya bayyana cewa kasar Saudiyya na da mutane Miliyan 34 a yayin da Najeriya ke da mutane…

Read More

Da Yiwuwar A Rage Farashin Mai A Najeriya

Kamfanin kasuwancin kayayyakin arzikin man fetur a Najeriya (PPMC) na iya rage farashin man fetur a cikin wannan watan. A hira da aka yi da mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandu, ya bayyana cewa ‘yan kasuwan na kyautata zaton za’a rage farashin man a watan Oktoba. Ya bayyana hasashensa ne bisa ga saukar farashin mai a kasuwar duniya. Farashin yanzu ya sauko $39.38. Amma ya ce sai kamfanin PPMC ta sanar da sabon farashin zasu fara sayarwa. Amma hukumar lura da farashin…

Read More

Hukumar Ya?i Da Rashawa Ta Banka?o Bada?ala A Shirin Ciyar Da Yara

Hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta (ICPC), a ranar Litinin, ta ce ta bankado makuden kudi har N2.67 biliyan na ciyar da ‘yan makaranta amma a asusun bankuna masu zaman kansu. ICPC ta ce kudin da aka waskar zuwa asusun bankuna masu zaman kansu, an bada ne domin ciyar da yara ‘yan makaranta amma kuma suna gida. Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin taron gangami a kan yaki da rashawa a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Farfesa Owasanoye ya ce an bankado…

Read More

Shugaban Kasa Zai Rusa Kamfanin NNPC

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin sake fasalin Kamfanonin matatun mai na shekarar 2020 (PIB) a gaban ‘yan majalisar tarayya. Rahoton ya bayyana cewa wannan kudiri zai bada damar kafa sabon kamfanin man Najeriya. A dalilin haka kuma za a yi fatali da kamfanin man NNPC. Idan wannan kudiri ya samu karbuwa kuma har ya zama doka, gwamnati za ta soke hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya. Wannan kudiri ya ba Ministocin kudi da na man fetur ikon ganin yadda za ayi gwanjon dukiyoyi…

Read More

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Titin Dogo Daga Kano Zuwa Nijar

Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi fashin baki kan kwangilar ginin layin dogo daga Najeriya zuwa jamhurriyar Nijar da gwamnatinsu ta bada. Mun kawo muku rahoton cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da fitar da Dallar Amurka biliyan 1.95 domin ginin layin dogo da zai tashi daga Kano-Dutse (Jigawa)-Katsina-Jibia zuwa Maradi (Jamhuriyar Nijar). Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a gidan gwamnati bayan taron Majalisar da Shugaba Buhari ya jagoranta a…

Read More

Farashin Mai Da Lantarki: ?ungiyar ?wadago Ta Sanya Ranar Zanga-zanga

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ta ce ba za ta fasa zanga zangar da ta shirya yi ba daga ranar 28 ga watan Satumban 2020 bayan gwamnatin tarayya ta ki mayar da tsohon farashin man fetur da lantarki a kasar. Kwamared Wabba ya ce dukkannin shugabannin kungiyoyin na jihohin Najeriya 36 da na Abuja sun amince da fara yin zanga-zangan daga ranar 28 ga watan Satumba. Ayuba Wabba ya ce kungiyar za ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi mako mai zuwa bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwar Kungiyar…

Read More

Ku Guji Kar?ar Bashi Domin Ayyuka – Sunusi Ga Gwamnatoci

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnatoci su daina karban bashi domin aiwatar da ayyuka. Hakazalika ya bayyana cewa rashin neman wata hanyar kudin shiga sabanin man fetur tsawon shekaru 60 yanzu ya haifar da halin talaucin da ake ciki yau. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce maimakon karban bashi, kamata yayi gwamnatoci su zuba kudi wajen gina mutane da kuma manufar janyo hankalin masu sanya hannun jari. Ya bada wannan shawara ne a taron sanya hannun jarin da gwamnatin jihar Kaduna ta shirya ranar Talata.“Yayinda…

Read More

Kimanin Matasa 2000 Ne Za Su Samu Aiki ?ar?ashin Bizi Mobile

An ?iyasta cewa kimanin Matasa 2000 ne zasu samu gajiyar aikin Banki da Kamfanin Bizi Mobile, kamfanin da ya saba hada hadar ku?i ta zamani. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban Kamfanin Alhaji Aminu Bizi, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna. Bizi ya bayyana cewar tuni kamfanin nashi bisa ga ha?in gwiwa da babban Bankin Najeriya,suka cimma wata matsaya na inganta rayuwar matasa da magance matsalar zaman banza, kuma kamfanin nashi ya bada fifiko sosai a yankin Arewacin Najeriya, kasancewar yankin na koma…

Read More

Gwamnati Ta Bukaci Jama’a Su Cike Takardun Bayanan Kai Da Kai Daga Bankuna

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya masu asusun ajiye kudade a bankuna ko kamfanonin inshora da su gaggauta karbar takardun cike bayanan kai wato ‘Self-Certification Forms’. A cewar sanarwar da gwamnatin tarayyar ta fitar ta shafinta na Twitter a ranar Alhamis, ta ce bayan cike takardun, a mayar da su ga bankuna ko kamfanonin ajiye kudaden. Ga wadanda ke amfani da asusun ajiye kudin a bankuna daban daban, sanarwar ta ce dole su cikewa kowanne banki wadannan takardu, su mayar da takardun ga kowanne banki. A cewar…

Read More

Kwanan Nan ‘Yan Najeriya Zasu Fara Shan Fetur Da Sauki – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za a fara sayar da man fetur a farashi mai matukar sauki, wanda jama’a za su dara. Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a karamar hukumar Egbema da ke jihar Imo yayin rangadin da ya je karamar matatar man fetur da za a kaddamar a wata mai zuwa. Da irin wannan matatun, ministan ya ce dukkan magana a kan tallafin man fetur zai zama maras amfani saboda za a dinga samunsa…

Read More

Kada Ku Karya Tattalin Arzikin Najeriya Da CORONA – Majalisar Dattawa

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan da kada su kashe tattalin arzikin Najeriya ta hanyar daukar salon Turawa wurin yaki da annobar korona. Majalisar dattawan ta yi wannan zancen ne a ranar Talata sakamakon sabon salon yaki da cutar korona da aka dauka. Sun samu zantawa tsakanin kwamitin majalisar dattawa da ke kula da sufurin jiragen sama da lafiya, da kuma masu ruwa da tsaki a kan yadda cutar korona ta kasa kamari a Najeriya da sauran kasashen Afrika. Shugaban…

Read More

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Gidajen Kallon ?wallo

Hukumar Tara Ku?a?en Haraji na Jihar Kaduna ta rufe wasu manya-manyan gidajen buga cacan kwallon kafa da ke jihar. Hukumar ta ce gwamnatin jihar na bin wadannan gidajen buga cacan kwallon kafa dake kasuwanci a jihar da suka hada da Betnaija, BetKing, Acesss Bet da sauransu. Shugaban sashen gidajen buga wasannin da caca, Liye Anthony ya bayyana cewa akwai akalla gidajen cacan kwallon kafa 1500, kuma za su bisu daya bayan daya su gar?ame saboda basu da cikakken rajista da gwamnatin jihar sannan ana bin wasunsu miliyoyin ku?in haraji da…

Read More

‘Yan Kasuwar Da Suka Ci Bashinmu Sun Yi ?atan Dabo – Gwamnatin Tarayya

‘Yan Kasuwan da aka baiwa bashin jari karkashin shirin ‘Trader Moni’ da gwamnatin tarayya ta shirya karkashin ma’aikatar jin dadin da walwalan al’umma domin rage talauci, sun ki biya. Jagorar shirin NSIP ta jihar Kwara, Hajiya Bashirah AbdulRazaq-Sanusi, ta bayyana hakan ranar Laraba, kamar yadda The Punch ta ruwaito. Hajiya Bashirah tace kimanin mutane 10,000 suka samu bashin ‘Trader Moni’ a jihar idan aka raba musu kimanin bilyan 1.3. Ta ce abin damuwan shine mutanen na ikirarin cewa ba zasu biya ba. Talakawa basu shirya biyan bashin da aka basu…

Read More

Kotu Ta Haramtawa Kantin “Shoprite” Kwashe Kadarorin Sa

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Lagos, ta ki sauraren uzirin neman janye maganar da ta yi wa katafaren kantin zamani, Shoprite, wanda ta hana ya kwashe kadarorin sa daga Najeriya, saboda ana bin sa bashin dala milyan 10. Shoprite ya garzaya kotu inda ya nemi Mai shari’a ya janye ?aurin-talalar da ya yi wa kantin na hana shi wasu mu’amaloli da Kadarorin na sa. Mai Shari’a Nicholas Oweibo, ya ce tunda yanzu kotuna duk hutu su ke yi, ba zai iya sauraren bukatar Shoprite ba, sai dai ya…

Read More

?arin Farashin Mai Ya Tabbata Ba Za A Rage Ba – Buhari

Shugaba Buhari ya ce ba a za rage ?arin ku?in litar man fetur ba, domin idan gwamnati ta ci gaba da biyan tallafin rarar mai, to tattalin arzikin Najeriya zai shiga garari nan gaba. Mataimakin Shugaban ?asa ne ya sanar da wannan bayani, a madadin Shugaba Buhari, yayin da ya wakilce shi a taron kwanaki biyu na Bitar Ayyukan Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Na Shekara-shekara, a ?akin Taro na Fadar Shugaban Kasa. Buhari ya ce annobar cutar Korona ta dankwafar da ?arsashin da tattalin arzikin ?asar nan ke da shi, ta…

Read More

Bu?e Boda Ne Mafita Akan Tsadar Shinkafa – Rimingado

Hukumar kar?ar ?orafe-?orafe da ya?i da rashawa ta Kano, tace ta yi iya ?o?arinta wajen ganin ta magance ta’azzarar farashin shinkafa, sai da a wannan karon abin ya ci tura. Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimingado ya ce ba zasu iya daidaita farashin shinkafa ba a yanzu domin matsalar ba daga masu samar da shinkafar ba ne. “Hana shigo da shinkafar da gwamnatin tarayya tayi shine musabbabin da ya haifar da tsadar shinkafar, kuma gwamnatocin jihohi ba zasu iya ta?uka komai a kai ba. “Gwamnatin tarayya ce ka?ai za ta iya…

Read More

‘Yan Najeriya Sun Koka Akan Hauhawar Farashin Mai Da Lantarki

Kungiyar Kwadago da kuma sauran al’umma a Najeriya musamman a kafafen sada zumunci na zamani sun bayyana matukar damuwa da mamakinsu dangane da yadda mahukuntan kasar suka yanke shawarar kara farashin wutar lantarki da kuma na man fetur a lokaci daya. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da bayyana damuwa dangane da yanayin fatara da suka tsinci kansu a fadin kasar na matsin tattalin arziki. Ko a jiya jaridar muryar yanci ta kawo maku ruhoton babban labarin ta inda shugaban kasa Muhammadu Buhari…

Read More

?arin Farashin Mai: Shukar PDP Ce Muke Girba – APC

Jam’iyya mai mulki ta (APC) ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam’iyyar adawa ta (PDP) da gwamnatocinta na baya. Jam’iyyar APC ta yi raddi ne ga PDP yayin data a soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin halin talauci. APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu. Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan…

Read More