Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya kare shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan hada Najeriya da kasar Saudiyya da yayi akan farashin Man fetur.
A jawabinsa na ranar ‘yanci shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai kamata ace Najeriya na sayar da mai a arha fiyr da kasar Saudiyya ba.
Wannan magana ta jawo cece-kuce sosai a shafukan sada zumunta dana zahiri.
Saidai a karewar da yawa shugaban kasar, Lai Muhammad ya bayyana cewa kasar Saudiyya na da mutane Miliyan 34 a yayin da Najeriya ke da mutane Miliyan 200.
Yace sannan ganga Miliyan 10 Saudiyya ke fitarwa kullun ta man fetur amma Najeriya gabga Miliyan 2.1 take fitarwa.
Yace wadannan dalilai ne suka sa kasar Saudiyya ke iya biyan Albashi me kyau fiye da Najeriya. Ya yabawa kungiyar kwadago da ta janye yajin aiki.
