Kotun shari’ar Musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a a Jihar Kano ta bayar da umarnin kamo mata Jarumin wasan Hausan, Sadiq Sani Sadiq.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa wani mai shirya fina-finai, Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da ?arar a gaban kotun, inda ya ke ?orafin cewar ya baiwa jarumin ku?i domin ya yi masa aikin film, amma ya?i zuwa don yin aikin.
Mai ?arar ya kuma yi ?orafin cewa ?in yi aikin da Sadiq ya yi ya ja masa asara mai yawa.
Alkalin Kotun, Maishari’a Sagiru Adamu, yace Sadiq ya bijirewa umarnin kotu duk da sammacin da aka bashi, tare da li?e masa sammacin a bangon gidansa, amma yaki halartar zaman kotun.
Shine sai ya baiwa dan sandan kotun umarnin kamo jarumin a duk inda yake zuwa gaban kotun.
Kotun tace da zarar an kamo jarumin wasan Hausan za a cigaba da zaman sauraren shari’ar.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Sadiq ya ce ba mai shirya fim ?in ba ne ya bashi ku?in kai tsaye.
Sadiq ya ?ara da cewa Naira dubu ?ari a ka bashi a matsayin wani ?angare na ku?in kwantaragin fim ?in.
In da ya ce shi ba cinye masa ku?i ya yi ba, hasali ma bai san ko wanene mai fim ?in ba tunda ba kai tsaye su ka kulla yarjejeniya ba.
