Rundunar Ya?in Neman Za?en Tinubu ta fitar da sabuwar tantebur ?in kamfen, wadda a ciki aka tabbatar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai taya shi kamfen a?alla a jihohi 10.
Festus Kiyamo ne ya fitar da wannan sanarwar tare da sa mata hannu a ranar Juma’a.
Keyamo ya ce Buhari zai ?aga wa talakawa tsintsiya a ranar 9 Ga Janairu a Adamawa, 10 ga Janairu a Yobe, 16 Ga Janairu a Sokoto, sai kuma Kwara a 17 Ga Janairu. Ogun kuma a ranar 17 Ga Janairu.
Keyamo ya ?ara da cewa Buhari zai halarci kamfen a Kuros Riba, a ranar 30 Ga Janairu, Nasarawa a ranar 4 Ga Fabrairu, Katsina a 6 ga Fabrairu, sai Imo a ranar 14 Ga Fabrairu.
Haka kuma Buhari zai halarci kamfen ?in TInubu na ?arshe a ranar 18 Ga Fabrairu a Legas.
Tun da Buhari ya halarci ?addamar da kamfen ?in TInubu a ranar 15 Ga Nuwamba, 2022 a Jos bai ?ara fita kamfen ?in TInubu ba.
Hakan ya sa an ri?a nuna damuwa cewa Buhari bai damu da Tinubu ya ci za?e ko ya fa?i za?e ba.
“Rundunar Ya?in Neman Za?en Tinubu/Shettima na murna ganin Shugaba Muhammadu Buhari zai ?ara mata ?warin-guiwar fitowa ya taya ta kamfen a jihohi 10. Wannan kuma zai ?ara wa kamfen ?in karsashi sisai.
“Mu na kira ga ?aukacin magoya bayan APC su ri?a fitowa ?wai da kwarkwata wurin ya?in neman za?e.
Yayin da wasu ke jinjina wa irin namijin ?o?arin da Tinubu ya yi domin ganin Buhari ya yi nasara a za?en 2015, ana kallon cewa a yanzu shi Buhari bai nuna masa irin haka ba.
