Aikin Soja Ba Sana’ar Neman Kudi Bane – Shugaban Dakarun Soji

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Faruk Yahaya ya bayyana cewa masu han?oron shiga aikin soja su saka a ran su cewa za su shiga ne domin kishin ?asa da sadaukarwa gare ta, amma su daina yi wa aikin soja wani wurin samun aiki.

Ya ce aikin soja aiki ne na kare Najeriya, ba wurin aikin samun ku?i ba ne.

Laftanar Janar Yahaya ya yi wannan nunin a lokacin da ake wa masu neman shiga aikin kuratan sojoji gwanin juriyar gudun kilomita 10.

An ?addamar da yi masu gwajin ne a Cibiyar Gwajin Horon Sabbin Suratan Sojoji da ke Dajin Falgore, Jihar Kano.

Wannan bayani na Laftanar Janar Yahaya na ?unshe a cikin wata sanarwar da Kakakin Hul?a da Jama’a na Sojojin Najeriya, Onyema Nwachuku ya fitar a ranar Asabar, a Abuja.

Ya ce shiga aikin soja ba kamar samun aiki ba ne a wasu fannoni na rayuwa, shi aikin soja aiki ne na sadaukarwa ?ungurugum wajen kare Najeriya.

Ya ce wa?anda ake bu?ata su shiga aikin soja, su kasance lafiyar su garau, jikin su gagau, ganin su ranga?au, ?wa?walwar sa?ai ta ke babu wani dattin ta?in hankali, wauta, buguwa, gargajiganci ko kuma alamomin ?abi’un shagirigirbau a jikin mutum.

“Aikin soja ba aiki ne da kowane ke iya shiga ba. Ba wurin neman ku?i ba ne. Aiki ne na sadaukar da rayuwa domin a kare ?asa kawai.”

Daga nan Yahaya ya shawarci masu neman shiga aikin soja ?in su ?auki wannan tantancewa da ake yi masu da muhimmancin gaske.

Related posts

Leave a Comment