DAGA BASHIR ADAMU, JALINGO
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Taraba na cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar wato Rt Hon Joseph Albasu Kunini yayi murabus daga mukaminsa, a safiyar ranar Laraba, 21-12-2023.
An bayyana murabus din Kakakin Majalisar ne a wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin Jihar a ranar Larabar inda Mataimakin Kakakin Majalisar Hamman Adama Ibn Abdullahi ya karanta a Zauren Majalisar wanda kuma shine ya jagoranci zaman majalisar. Wasikar na kunshe da cewa Albasu Kunini yayi murabus din ne bisa kudirin kansa.
Tuni dai yan Majalisar suka maye gurbin tsohon Kakakin Majalisar da Babban Mai Tsawatawa, kuma Shugaban kwamitin Ilimi a Majalisar, Rt. Hon. John Kizito Bonzena wanda yake wakiltan Mazabar Zing a majalisar Jihar ta Taraba, a matsayin sabon Kakakin nasu.
Da yake yiwa manema labarai jawabin jim kadan bayan kammala zaman Majalisar, sabon Kakakin Majalisar, Bonzena yace yin murabus din da tsohon kakakin ya yi ba zai shafi harkokin siyasar Jihar ba. Yana mai cewa, Kunini ya yi murabus din ne bisa muradin kansa, amman har yanzu shi membane a majalisar dokokin Jihar. Kuma zasuyi dukkanin abunda ya kamata domin ganin sun gudanar da ayyukan cigaban Jihar a tsakanin watanni kalilan din da suka ragewa Majalisar.
