Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar a wani bangare na ziyarar aiki na kwanaki 2 a jihar Kaduna da zai fara a ranar yau Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Kafanchan da ke Kudancin Kaduna da sauran manyan garuruwan jihar domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka.
Buhari zai kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Kaduna, wadda za ta fara yau Alhamis kuma za ta kare a ranar Juma’a, in ji sanarwa daga gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim.
A cewar sanarwar: “Shugaban zai ziyarci manyan garuruwa uku na Kaduna, Zariya da Kafanchan, za kuma a nuna mishi ayyukan tituna a fadin jihar, wanda gwamnatin gwamna Nasir El Rufa’i ta aiwatar.”
Mai ba Gwamna El-Rufai shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya bayyana ayyukan da za a kaddamar da su hade da dandalin Murtala Muhammed da aka gyara, wanda ke tsakiyar garin Kaduna.
Mashawarcin na musamman ya kuma ce har da asibitin cututtuka masu yaduwa, wanda ke Mando, da kamfanin Dangote Peugeot Automobile Nigeria Limited daura da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, da kuma kasuwar Sabon Gari da ke Zariya.
Adekeye ya kuma ce shugaban zai kaddamar da wasu ayyuka kamar gadar sama ta Kawo da aka sake ginawa wadda ke da manyan kusurwowi guda uku da hanyoyin shiga, titin WAFF.
