Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana game da halin rashin tsaro da ake ciki, Malamin yace duk abin da ke faruwa yau, an fuskanci abin da ya fi haka a baya.
Shugaban kungiyar Jamaatu Izalatil Bida Waikamatis Sunnah ?angaren Jos ya bada shawara, ya yabi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.
Malamin yana ganin duk da kalubalen da gwamnatin nan take fuskanta na tsaro, yace Muhammadu Buhari ya zarce sauran shugabannin da suka shude a baya.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan ne a wajen taron gasar Al-Qurani musabaqa na kasa da aka shirya a garin Gombe. Yace
Muna fama da manyan matsaloli na rashin tsaro a kasar nan, amma nayi imani cewa halin da ake ciki ya fi yadda ake a baya. Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir.

