Buhari Ya Umarci Ministan Ilimi Ya Yi Gaggawar Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi Malam Adamu Adamu da ya kawo ?arshen yajin aikin malaman jami’o’in ?asar.

An ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin da ya sasanta abubuwan da ake ta?addama a kai cikin mako biyu sa’annan a kai masa rahoto.

A ranar Talata Shugaba Buharin ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki wa?anda ke da ala?a da ?angaren ilimi a ?asar da za su iya warware wannan tirka-tirkar.

Shugaban ya kira su ne domin ya samu ?arin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ?i ci ya ?i cinyewa.

Related posts

Leave a Comment