Mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya taya shugaban kasar Amurka Joe Biden da al’ummar Amurka murnar bikin ranar samun ?ancin kan Amurka.
Buhari ya ce yana kuma nuna goyon baya ga gwamnatin shugaba Biden kan yadda ta ke ko?arin magance manyan ?alubalen da Amurka ke fuskanta da suka ha?a da nuna wariyar launin fata da kuma ya?i da annobar korona da ta addabi Amurka, ?aya daga cikin ?asashen da cutar ta fi yin kisa.
Sannan ya ce yana cike da sha’awar yadda gwamnatin Biden ke ?o?arin inganta ala?ar Amurka da ?asashen Afrika da kuma tabbatar da ci gaban nahiyar, tare da bayyana fatan hul?ar Amurka da Najeriya za ta ci gaba da bun?asa domin amfanin mutanen ?asashen biyu.
