Buhari Ya Kalubalanci Hukumomin Tsaro Su Kara Kaimi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sake jaddada kira ga hukumomin tsaro da su kara azama wajen kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malama Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce za a kawo karshen ayyukan ta’addanci da na ‘yan bindiga ne kadai idan jam’an tsaron suka kara matsa kaimi.

Sanarwar ta kara da cewa duka ‘yan bingidar da suka addabi kasar za su dandana kudarsu.

Daga karshe Shugaban kasa Buhari ya yi wa ‘yan kasar addu’ar samun damina mai albarka.

Related posts

Leave a Comment