Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Alhaji Ibrahim Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Masari ya tabbatar da hakan ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli.
“Wannan don sanar da shugabannin jam’iyyarmu karkashin jagorancin Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, mambobin jam’iyyar da kuma mutanen Najeriya, sakamakon tattaunawa mai muhimmanci da na yi da mai rike da tutar jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
“Ku tuna cewa na samu alfarma inda aka zabe ni a matsayin abokin takarar Asiwaju Tinubu a watan da ya gabata bayan fafatawar da aka yi a zaben fidda gwanin shugaban kasa gabannin zaben 2023. “Amma bayan tattaunawa mai zurfi, a yanzu ina sanar da ku na janye.
