Babban Jigon jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Benuwai, Terhemba Ishegh, yace shugaba Buhari ya cika mafi yawan al?awurran da ya ?auka yayin yakin neman za?ensa ga yan Najeriya, kuma ya kamata ‘yan Najeriya su nuna godiyarsu bisa ga hakan.
Mr. Ishegh, wanda tsohon sakataren dindindin ne a jihar Benuwai, ya fa?i hakane yayin wata hira da yayi da Kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN) a makur?i.
Yace Buhari ya kafa ayyuka da dama duk da ?alubalen tsaron da ?asar nan ke fama da shi, amma duk da haka gwamnatinsa ba ta yi ?asa a guiwa ba har sai da ta cimma nasarori da dama.
A cewarsa, gwamnatin Buhari ta samu nasarori da dama a ?angaren kayayyakin gwamnati, ilimi, tattalin arziki da kuma ya?i da cin hanci da rashawa. Buhari ya kafa tarihi Ishegh ya ?ara da cewa duk da halin kakanikayi da kasar nan ta fa?a, gwamnatin Buhari tayi kokari wajen aiwatar da manyan ayyuka a fa?in Najeriya.
“Buhari ya yi namijin kokari a mafi yawan yankuna, wasu yankunan ya fara zuba musu ayyuka amma sai wasu matsaloli su hana karisawa.” “A jimulla zan iya cewa shugaba Buhari ya kafa tarihin da babu wani shugaban Najeriya da ya taba yi a cikin shekaru shida.”
“A halin yanzu, duk da ?alubalen tsaron da ake fama da shi kala daban-daban a yankunan Arewa-yamma, arewa-gabas, da arewa ta tsakiya sannan ya matsa zuwa kudu-yamma kudu-gabas.” “Amma gwamnati bata yi ?asa a guiwa ba ta cigaba da yin iyakar kokarinta wajen kawo karshen matsalar a wa?annan yankuna,” inji shi.
Mr. Ishegh, yace idan ma aka cire shirye-shiryen da gwamnati ta kirkiro na walwala da jin da?i ga talakawan Najeriya, Buhari ya samu damar aiwatar da muhimman ayyuka a kowane sashin ?asar nan.
Ya bayyana irin wa?annan muhimman ayyuka da suka hada da hanyoyi, gada, makarantu da kuma garambawul ga ?angaren samar da hasken wutar lantarki domin ha??aka tattalin arzikin ?asa.
