Sauya Takardun Kudi: Babban Banki Ya Jefa ‘Yan Najeriya A Talauci – Gwamnoni

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF ta sanar da cewar kasar ta kama hanyar fadawa matsalar tattalin arziki sakamakon shirin sake fasalin nairar da Babban Bankin kasar na CBN ya kaddamar.

Bayan wani taron gaggawa da gwamnonin 36 suka gudanar a karshen mako, shugabansu Aminu Waziri Tambuwal yace sun nuna bacin ransu akan yadda Babban Bankin ke aiwatar da shirin sake fasalin nairar da kuma rarraba shi, ganin yadda karancinta ya jefa ‘yan Najeriya cikin mummunan yanayi.

Gwamnonin sun ce babu wata shaidar dake tabbatar da ikrarin Babban Bankin cewar takardun kudade sun yi yawa a hannun jama’ar kasa sakamakon karin kusan naira trililiyan guda da rabi da aka samu a shekarar 2015, abinda ya kaiga kudaden dake hannun jama’a sun kai naira triliyan 3 da biliyan 230 a watan Oktobar bara.

Kungiyar gwamnonin tace Babban Bankin bai yi la’akari da habakar kudin shigar da aka samu na GDP ba a wannan lokaci da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da karuwan yawan jama’ar kasa ba kafin yanke hukuncin.

Gwamnonin sun ce rashin samun wadatattun sabbin takardun kudaden ya bada damar sayar da su ta bayan fage abinda ke haifar da hauhawar farashin kayayyakin abinci da kayan amfanin jama’a da kuma dogayen layuka a wuraren cire kudin dake bankuna na ATM, yayin da jama’a ke neman daukar wani kaso na kudaden ajiyarsu domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Kungiyar gwamnonin tace wannan hali da kasar ta shiga ya nuna karara cewar tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar durkushewa, kuma babu wanda alhaki ya rataya a wuyansa da ya wuce Babban Bankin Najeriya na CBN.

Related posts

Leave a Comment