Zaben 2023: Ko Da Sauyin Kudi Ko Babu Na San Lashe Zabe – Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce tun asali dama yana da ?warin gwiwar samun nasara a za?en shugaban ?asa da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata, duk kuwa da tsarin sauyin ku?i da CBN ya ?ullo da shi.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa a ziyara da ya kai wa sarakunan gargajiya na jihar Ogun da ke kudu maso yammacin ?asar.

Yayin da yake magana kan matsalolin da ya fuskanta a za?en shugaban ?asar da ya kai shi ga nasara, Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matakin ta?aita yawan ku?i da batun sauyin ku?i da CBN ya ?ullo da shi, wanda Tinubu ya ce ”bai yi nasara ba”.

Tinubu ya kuma gode wa sarkin Ijebu bisa shawarar da ya ba shi, game da yadda zai ?ullo wa ?alubalen a lokacin da ya ziyarci fadarsa a baya.

Related posts

Leave a Comment