Chushe A Kasafin Kudi: Majalisa Ta Dakatar Da Sanata Ningi Tsawon Watanni Uku

IMG 20240309 WA0082

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku

Abdul Ahmad Ningi dai shine shugaban Sanatocin Arewa kuma ya sako Gwamnati Tinubu a gaba kan Gazawar ta bisa mulki

Sai dai majalisar tace tana zargin Sanata mai wakiltar shiyyar Bauchi ta tsakiya da yin kalaman da ya danganta musu cushe cikin kasafin kudin 2024, lamarin da suka ce bai musu dadi ba kuma ba da yawun su yi yi ba.

Abdul Ahmad Ningi shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan al’umma kuma yana wakiltar Bauchi ta Tsakiya.

Shima Sanata ya fitar da takardar ajiye shugabancin Sanatocin Arewa.

Related posts

Leave a Comment