Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu

A kokarinta na dakile ayyukan ta’addanci a jihar Adamawa rundunan ‘yan sandan jihar tayi nasarar kama mutane sha hudu wadanda ake zargi da addabar gmazauna kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta kudu.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar ta Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

DSP Nguroje yace an samu nasarar kama wadanda ake zargin ne a samame da rundunan takai a wurare daban daban wanda hakan ya bata daman kama mutanen tare da Mota guda daya kiran Audi, Kwamfitoci 6 , TV 2 da miyagun kwayoyi da dai sauransu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Sikiru Akande ya tabbatarwa al’ummar jihar cewa rundunar a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin al’umma baki daya.

Don haka nema kwamishinan ya kirayi al’ummar jihar da su kasance masu ba Rundunar hadin kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na dakile ayyukan ta addanci a fadin jihar ta Adamawa baki daya.

A yayin gudanar da bincike wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa sune suka addabi mazauna garin Jimeta da Yola wajen shiga gida gida suna fashi tare da kwace Kayayyaki da dai sauransu.

Related posts

Leave a Comment