Borno: Zulum Ya Ro?i Buhari Ya Taimaka A Dawo Da ‘Yan Gudun Hijira Gida

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya ro?i gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin Shugaba ?asa Buhari ke jagora ta taimakawa ?an gudun hijiran Najeriya kimanin 200,000 da ke Nijar, Kamaru da Chadi su dawo gida.

Gwamna Zulum ya yi wannan rokon ne a ranar Juma’a a Abuja cikin jawabin da ya yi wurin taron masu ruwa da tsaki kan taimakawa ?an gudun hijirar Najeriya dake rayuwa kasashen makwabta.

Ya bayyana taron a matsayin abin yabawa da jinjinawa. “?an gudun hijira kimanin 200,000 ?an asalin jihar Borno da ke zaune a Kamaru, Chadi da Nijar suna son dawowa gida. Sun da?e suna neman a dawo da su gidajensu.
Sun sako ni a gaba. Ina ro?on gwamnatin tarayya ta taimaka.

Related posts

Leave a Comment