Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i, a cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma’a, ya sanar da cewa ya killace kansa, domin tsaro ba domin tsoro ba, saboda kariya daga bahaguwar cutar nan ta CORONA, wadda ake zargin ta sake dawowa.
El-Rufa’i, ya sanar da cewa ya sake killace kansa bayan wasu na hannun damansa da hadimansa sun kamu da kwayar cutar korona, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma’a. A cewarsa, ya killace kansa ne biyo bayan samun rahoton cewa wasu na hannun damarsa da makusanta iyalinsa sun kamu da kwayar cutar korona, kuma sun yi cudanya kafin fitowar sakamakon gwajinsu.
A ranar Alhamis ne El-Rufa’i ya ce akwai yiwuwar zai sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa.
Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa’i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan.
