Babu Likitan Da Ya Shawarci Tinubu Ya Aje Takara – Makusanta

Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Joe Igbokwe, daya cikin na hannun daman Asiwaju Bola Tinubu, ya yi martani kan ikirarin da wani Maxwell Nwadike ya yi na cewe likitan dan takarar shugaban kasa na APC ya shawarce shi ya ajiye takararsa na 2023.

A cewar Nwadike a wani rubutun da ya yi a Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa yanayin lafiyar Tinubu a halin yanzu ne yasa likitansa ya bashi wannan shawarar.

Da ya ke magana kan ikirarin, Igbokwe a wani rubutu da ya yi a Facebook a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta, ya bayyana batun a matsayin tsantsagwaran karya. Igbokwe ya fayyace cewa “labaran bogi, farfaganda, zagi, bita da kulli da sauransu ba za su taimakawa kowa cin zaben shugaban kasa na 2023 ba.”

Ya ce abin da kawai zai iya taimakawa mutum cin zabe sune ‘ayyukan kirki da mutum ya yi a baya, kwarewa, ilimi, zumunci, kusantar talakawa, sanin mutane a kasa da kasashen waje, magoya baya da abota da aka gina na tsawon shekaru’.

Igbokwe ya kammala rubutunsa na Facebook da cewa: “Asiwaju ya dade yana aiki kuma yana shirin darewa kujerar shugaban kasa tun kafin shekarar 1993 …”.

Related posts

Leave a Comment