Daga karshe Bishop na Katolika da ke Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya fayyace biri har wutsiya kan cece-kucen da sakonsa na Kirsimeti ya haifar, inda ake ya?a cewar ya yi kira da a yi wa Buhari juyin mulki.
An ruwaito cewa babban faston ya ce shi bai yi kira ga juyin mulki ba a sukar da yayi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda wasu rahotanni suka ya?a, inda ya bayyana cewar kawai dai ya fadi ra’ayinsa ne bisa hujja.
An tattaro cewa yayinda ya ke zargin Buhari da son kai a sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, faston ya ce idan da ace Musulmin da ba dan arewa bane ya aikata abunda Buhari ya aikata, to da an yi masa juyin mulki.
Da yake zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin, 28 ga watan Disamba, Kukah ya ce babu adalci a rahoton cewa shi ya nemi ayi juyin mulki.
“Babu adalci wani dan jarida ko wata kafar labarai ta ruwaito cewa na yi kira ga yin juyin mulki yayinda na bayyana ra’ayina game da Najeriya.”
Kan kira ga cewar ya ajiye limancinsa sannan ya shiga siyasa, malamin ya ce idan da zai shiga siyasa, toh da ya shige ta a zamanin marigayi Aminu Kano amma ba a yanzu ba.
Kukah ya kara da cewa shi baya shirin sanya kansa a siyasar bangaranci, cewa masu alakanta sakonsa da siyasar bangaranci na zargi ne mara tushe.
Ya ce duk abin da ya fadi yana iya da?a?awa mutum ko ya bata masa, inda ya kara da cewa fadin nasa ra’ayin ba zai hana sauran mutane fadin nasu ra’ayin ba.
