Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno na nuna cewa mayakan Boko Haram sun zafafa hare -haren da suke kai wa wasu yankunan jihar a baya-baya nan.
Rahotannin sun ce akalla mutum biyar ne suka mutu a wani hari da ake zargin mayakan da kai wa kan wani ?angare na garin Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Mayakan sun kuma jikkata mutane 11.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaida wa BBC cewa a daren juma’a ne mayakan suka kai harin inda suka harbo roka daga bayan gari.
“Yanzu an yi jana’izar mutane biyar da suka mutu, kuma 11 da suka ji ciwo, jami’an kungiyar agaji ta Red cross sun taimaka sun kawo helikwafta suka kwashe wadanda aka raunata da ke cikin mawuyacin hali”.
