Tsohon shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, ya bayyana hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da shi daga rike mukamin gwamnati har zuwa 2030 a matsayin cin amana.
Kotun ta same shi da laifin yin amfani da karfin ikonsa na shugaban kasa zamanin da yake mulki.
A yayin wani jawabi da ya yi ne wanda aka yada ta talabijin a watan Yuli na bara, inda a lokacin ya nuna shakku kan sahihancin tsarin zaben kasar ta hanyar kwamfuta ba tare da ya nuna wata sheda mai karfi ta zargin magudi ba.
Mista Bolsonaro ya ce yana tunanin daukaka kara, kuma zai ci gaba da fafutukar neman ‘yancin Brazil.
