?ungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu da kuma masu dakon man sun musanta yun?urin ?ara farashin man zuwa N700 kan lita ?aya.
Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) ta masu kasuwancin mai da kuma Distributors and Transporters of Petroleum Products (ADITOP) sun musanta shirin ne cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar.
Suka ce farashin mai a yanzu yana tafiya ne kan farashin kasuwa, kuma an yi hasashen ?ara ku?in man ne saboda darajar naira da ke sama tana ?asa a kasuwar canji.
A cewar rahoton NAN, wasu ‘yan kasuwa sun yi hasashen tashin farashin man ne zuwa naira 700 kan kowace lita, sa?anin yanzu da yake 540, da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun fara shiga da man cikin ?asar a watan Yuli.
