Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaban ?asa Mhammadu Buhari ya yi “amfani da dukkan ?arfinsa” wajen kawo ?arshen matsalolin tsaro da ke addabar sassan ?asar.
Majalisar ta yi kiran ne cikin wata matsaya da ta cimma yayin zamanta na ranar Laraba.
Babu bayani kan ko sau nawa majalisar ta yi irin wannan kira yayin da gwamnatin ke cewa tana bakin ?o?arinta.
Wani rahoto kan sha’anin tsaro da kamfanin Beacon Consulting ya fitar ya ce hare-haren ‘yan bindiga sun kashe mutum 1,500 cikin watan Maris ka?ai a Najeriya.
‘Yan bindiga ?ar?ashin ?ungiyoyi daban-daban kan kashe mutane ko kuma yin garkuwa da su don neman ku?in fansa a lungu da sa?o na ?asar.
