Sokoto: Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Bindiga Masu Yawa

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu gungun yan bindiga da suka yi kokarin sace mace mai juna biyu dakarun soji sun harbe su har lahira cikin gaggawa.

Daraktan ya?a labarai na ma’aikatar tsaro, Benard Onyeuko, shine ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar tsaro dake Abuja.

Yace dakarun rundunar sojin ?asa na operation hadarin daji sun ragargaji yan bindiga 14 dake aikata ta’addanci a ?auyen Aldabala, karamar hukumar Tangaza, jihar Sokoto. Onyueko ya kara da cewa sojojin sun samu nasarar ku?utar da mutane 35 daga hannun yan ta’addan.

Wani ?angaren jawabinsa yace: “Sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda bakwai, mashin guda shida, kayan sojoji da yan sanda, motoci 6 da dai sauran su.” “Hakanan kuma jami’an sojin sun taimakawa ?aya daga cikin wa?anda ?arayin suka yi kokarin sacewa ta haihu cikin koshin lafiya.”

Ya kara da cewa gwarazan sojojin sun damke masu taimakawa yan bindigan da bayanai mutum 16, da wani mayaudari da ya bayyana kansa da Corporal.

Jawabin ya kara da cewa: “Tsakanin 16 zuwa 29 ga watan Yuli, sojojin mu sun kai ?auki a kiran waya da aka musu kan harin yan bindiga da yan ta’adda a kauyukan Hanutaru da ?ansadau dake karamar hukumar Maru.” “A?alla yan bindiga 14 ne suka kashe yayin da suka ku?utar da mutane 36 da aka sace a cikin wannan lokacin.”

Related posts

Leave a Comment