Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC) daga gayyata ko cin zarafin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan bidiyon da ake zarginsa da karbar dala.
Hukumar PCACC a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ta sanar da cewar ta gayyaci tsohon gwamnan don ya amsa wasu tambayoyi kan binciken da take yi a kan bidiyon wanda ake zarginsa da karbar cin hanci daga dan kwangila.
Sai dai a wata kara da aka shigar gaban mai shari’a A.M. Liman, a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuli, tsohon gwamnan ya bukaci kotun da ta dakatar da wanda ake kara na takwas daga cin zarafi, tsoratarwa da gayyatar mai karar.
Haka kuma an bukaci kotun da ta dakatar da wanda ake karar daga yin barazanar kamawa da tsare wanda ke karar ko yaransa ko wani danginsa ko kuma wani da ya yi aiki karkashin gwamnatinsa ko kuma kwace kadararorinsa ko na yaransa ko danginsa ta karfin tuwo.
