Talauci Da Jahilci Ne Suka Haifar Da ‘Yan Bindiga A Arewa – Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima, ya yi ikirarin cewa talauci da jahilci ne ya haifar da ayyukan ta’addancin ‘yan bindigan jeji a Najeriya A makon da ya gabata, Yerima ya bu?aci gwamnati ta rungumi tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga domin kawon karshen zubda jini, garkuwa da mutane da sauransu.

Da yake hira da Channels tv cikin shirin Politics Today ranar Jumu’a, Yerima ya ce ingantaccen ilimi zai tsamo duk mai hannu daga aikata wa?an nan munanan ayyuka. “Babu wani mai ilimi, Musulmi ko kirista, Bayahude ko Hindu, wanda ke cikin hankalinsa kuma yana da aikin yi, bai ha?a hanya da talauci ba amma haka kurum ya ?auki makami ya kashe mutane.” “Babbar matsalar da ta yi wa irin wa?an nan mutanen katutu ita ce talauci da kuma jahilci.”

Yerima, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya ?ara da cewa gwamnatocin baya ba su ta?uka komai ba wajen da?ile ya?uwar yan bindiga. “A baya gwamnatocin jihohi ba su kula da su ba, kuma ga barayin shanu sannan filin kiyon da aka ware musu duk manoma sun ?wace,” inji shi.

Tsohon gwamnan ya kuma musanta ra?e-ra?in cewa ?umbin albarkatun kasa da ke Zamfara kamar zinare na daga cikin manyan abubuwan da suka taka rawa wajen ?aruwar ayyukan ‘yan fashin daji.

Related posts

Leave a Comment