Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Tinubu na shirin zama shugaban ?ungiyar raya tattalin arzi?in ?asashen Afirika ta Yamma (ECOWAS).
Shugaba Tinubu, wanda ya bar Abuja a ranar Asabar domin halartar taron shugabannin ?asashen, ana sa ran zai kar?i ragamar shugabancin ?ungiyar daga hannun Umaro Sissoco Embaló na ?asar Guinea-Bissau.
Taron karo 63 na shugabannin ?asashen za a gudanar da shi ne a birnin Bissau, babban birnin ?asar Guinea-Bissau.
Taron na shugabannin ?asashen da ke a ?ungiyar ECOWAS zai tattauna kan batutuwan da suka shafin yankin, da suka ha?a da matsalar tsaron da wasu daga cikin ?asashen ke fama da ita da batun tattalin arzi?i. Taron zai duba batun kaddamar da kasuwanci ba tare da wani shamaki ba a nahiyar Afirika da rahoto kan halin mi?a mulki a ?asashen Mali, Burkina Faso da Guinea.
