Uwar gidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed taja hankalin mata da su rage yawon Maula ko Kwaram a gun yan’siyasa, da bin kwararo-kwararo suna rokon mutane abasu na abinci ko wani abu makamancin haka.
Tayi wan nan jankunne ne a wajen taron tallafama al’ummar yankin karamar hukumar Ganjuwa da kayayyakin sana’oi dabam-dabam, wanda ya gudana a garin kafin madaki.
Aisha Bala tace yanzo lokaci yayi da mata zasu daina tsaya wa suna jira abasu saidai suma su bada tasu gudumuwar ta hanyar sarrafa kayayyakin tallafin da gwamnatin Bauchi ta basu bisa cika al’kawurran da suka dauka ma mutanen Jihar, yayin da suke neman kuriarsu a zaben gama gari da ya kawo su kan karagar mulki.
Uwargidan Gwamnan taci gaba da cewa
“Saninku ne mu mata mun iya saraffa kudi da naira dubu biyar, 5000 dubu goma 10,000 zamu iya kasuwanci, balle wacce aka bata naira dubu Hamsin 50,000, muna fata mata za suji tsoron Allah, muje mu kama sana’a, mu daina yawon kwaram wan nan sana’a idan kika rike shi tsakanin ki da Allah, bi’izinillahi ta’ala Allah zai sa mashi albarka”
“wata rana kece miloniya kene mai taimaka ma yayanki da makwabta da wadanda basu dashi musamman marayu a Jihar namu, kana tayi addu’a Allah ya kara ma Gwamnatin Jihar kwazon taimakawa ma al’umma daidai gwargwado” ta fada.
Kayayyakin da aka raba wa matan a wajen taron sun hada da injinan markade fiye da guda dari da kayan soyesoye na kana nan sana’oi mangyeda da kayan tallafin, da kuma kudade, acewarta kuwa ce mace ta zabi abunda take so tayi Alan haka akaba su kayan da suka zaba a matsayin tallafin don habbaka kasuwan cinsu a kana nan hukumomin su.
Daga Adamu Shehu Bauchi
