Adamawa: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gabatar Da Kayayyakin Da Ta Kama A Shekaru 2

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta gabatar da wasu kayaki wadanda ofisoshin rundunan dake Mubi ta kudu, Fufore, Kofare da kuma Ganye suka gano a tsakanin shekara ta 2019 da 2020 wanda kuma har ya zuwa yanzu na wanda yazo ya nuna cewa kayansa ne.

Rundunan dai ta gabatar da kayakin ne a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan wato D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a yola Fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Sanrawan ta cigaba da cewa kwamishinan yan sandan jahar ta Adamawa CP Aliyu Adamu Alhaji ya kirayi al umma musammanma wadanda akayi musu sata da suzo shelkwatar rundunan ta takardun cikekken bayanin cewa kayakin nasune domin karban kayansu.

Kwamishinan ya tabbatarwa al ummar jahar ta Adamawa cewa rundunan a shirye take ta kare rayuka dama dukiyoyin al ummar dake fadin jahar baki daya.

Harwayou kwamishinan ya kirayi daukacin al ummar jahar da su baiwa rundunan hadin kai da goyon baya domin ganin rundunan ta samu nasaran yakan ta addanci a tsakanin al umma baki daya.

Cikin kayakin da aka gabatar din dai sun hada da mashin, janareta, talabijin da dai sauransu.

Related posts

Leave a Comment