Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta za?i manyan ?wararrun lauyoyi 12 domin tsaya mata a shari’ar ?orafin da jam’iyyun adawa za su shigar domin ?alubalantar nasarar jam’iyar a za?en shugaban ?asa.
A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta hannun babban mai bayar da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar Ahmad El-Marzuq, ya ce tawagar lauyoyin masana fannin shari’a ne, wa?anda kuma ya ce suke da ?warewa kan ?ararrakin za?e, sannan masu cikakkiyar masaniya game da kundin tsarin mulki da dokokin ?asa.
Ya ce tawagar manyan lauyoyin12 ?ar?ashin jagorancin fitaccen lauyan ?asar Prince Lateef Fagbemi za su kare nasarar da jam’iyyar ta samu a za?en a gaban kotu.
Manyan jam’iyyun adawar ?asar na PDP da LP ne dai suka ce za su garzaya kotu domin ?alubalantar sakamakon za?en shugaban ?asar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara a za?en shugaban ?asar da aka gudanar cikin watan da ya gabata.
