Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai jagoranci shugabannin Afirka taron ECOWAS yau Lahadi a Abuja.
Taron da za a yi na shugabannin ?asashen shi ne na 60 kuma ana yin irin wannan taron a duk shekara.
Ana sa ran tattaunawa kan batun siyasa da tsaro da tattalin arzi?in ?asashen.
Haka kuma ana sa ran tattaunawa kan halin da ?asashen Mali da Guinea suke ciki.
