?an takarar gwamnan jihar Kaduna a ?ar?ashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP Isah Ashiru Kudan, ya bayyana hanyoyin da zai bi domin magance matsalar ?an bindiga a jihar. Ashiru Kudan ya bayyana cewa domin shawo kan matsalar, gwamnatin sa zata tattauna da ?ata garin domin samun maslaha inda yayi nuni da cewa su ma mutane ne ba dodanni ba.
Kudan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tashar talabijin ta ARISE TV, kan batutuwan da suka shafi nasarar jam’iyyar sa a za?en gwamna da na dan ?an majalisun jihar na ranar 18 ga watan Maris, 2023.
?an takarar na jam’iyyar PDP, ya soki wasu shirye-shirye na gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai, ciki harda korar wasu sarakunan gargajiya, inda ya ?ara da cewa hakan ya taimaka wajen ?ara ta?ar?arewar tsaro a jihar.
“Maganar gaskiya itace ko muna so ko bamu so, dole sai mun sanya mutane wajen ganin mun shawo kan wannan matsalar tsaron.” “Dole ne mu zauna da mutanen nan masu garkuwa da mutane. Mutane ne masu rayuwa a cikin mu. Mutane na tunanin cewa dodanni ne, ba haka bane. Zamu iya zama da su, mu tattauna da su, sannan mu kawo ?arshen wannan masifar.”
“Matsalar dake a Kaduna abin tashin hankali ne. Zo Kaduna ka gani. Mutane basu iya barci cikin kwanciyar hankali” “Idan har muna son mu kawo ?arshen wannan ta’adancin a cikin al’ummar mu, dole ne a zauna da mutanen nan domin tabbatar da cewa duk wata matsalar su an magance ta.
