Sukar Gwamnati: An Dakatar Da Sheikh Nuru Khalid Daga Limanci

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ?an majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid daga Limanci.

Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

A cikin hudubar, malamin ya fa?i matakin da ya kamata talakawa su ?auka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa za?e.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ?aya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito za?e ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” in ji Sheikh Nuru Khalid a hu?ubarsa.

A cikin wani sa?o da shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya fitar ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a.

Sanarwar ta ce: “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ‘?an Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.”

“An ?auki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi za?e a 2023 har sai ‘yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.”

Sanarwar ta ?ara da cewa “ya kamata a ce ka ba su shawara su fito za?e don kawar da wa?anda suka sa?a wa Allah, da masu za?e da kuma ?asa.”

Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta sa?a wa addinin Islama. Kuma a cikin sanarwar kwamitin ya na?a sabbin lamamai na Masallacin inda Malam Mohammad zai yi tafsiri, yayin da kuma Malam Abdullahi zai jagoranci Juma’a.

Babu wani martani daga Sheikh Nuru Khalid game da matakin da kwamitin ya ?auka na dakatar da shi, kuma BBC ta yi ?o?arin tuntu?ar malamin amma wayarsa a kashe.

Sheikh Nuru Khalid ya sha caccakar gwamnati kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, kuma hudubarsa na zuwa ne bayan harin da ?an bindiga suka kai wa jirgin ?asa a ranar Litinin inda aka kashe mutum takwas tare da sace mutane da dama.

A cikin hu?ubar Malamin ya ambaci wani da ke cewa “harakar tsaro ta zama kasuwanci a Najeriya, jinin talaka ya zama kayan kamfen a kasar nan, sai za?e ya kusa kashe kashe zai karu.”

“Mun dade muna hakuri – hanya ba kyau, talauci mun hakura, tsadar rayuwa mun hakura, karya mun hakura, kwashe kudin kasa mun hakura, ku bar mu mu zauna da ranmu kuma ba zai yiyu ba?”

Don haka a cewar Malamin abin da ya kamata talakan Najeriya ya yi shi ne ya ?auracewa za?e har sai an daina kashe rayukan al’umma.

Related posts

Leave a Comment