Kana nan yan’kasuwa a Jihar Bauchi sun roki gwamnatin Jihar data sake tunani kan wa’adin da ta kakabamasu na su kwashe kayansu a cikin awa arba’in da takwas, ko kuma su fuskanci fushin gwamnatin da bazai masu dadi ba.
Mu’azu Ciroma shine ya jagoranci wani gangami na lumana tare da nuna rashin jin dadinsu, inda sukayi tattaki daga Baban kasuwar zuwa sakatariyar Yan’jarida. akan wa’adin da kwamitin tsaftace chunkoson bakin kasuwanni da kan hanyoyi a fadin Jihar.
Yan’kasuwan suka ce wan nan lamarin ya tayar masu da hankali matuka, kuma basu da ikon yin wani abu face sukai kukansu a wajen Gwamnan Jihar Bala Abdulkadir Mohammed domin sake duba wan nan batu,
Suka kara da cewa sudai a sanin su tun a farkon al’amari ance su tashi Gwamnati ta basu sabon wuri a kusa da Kasuwar Muda Lawal, su ginashi a cikin wata uku, kachal don su koma, a cewarsu basu da karfin gina shagona a cikin wan nan kan kanin lokacin,
A dalilin hakan, suka kara da cewa suna son ayi masu adalci akara masu wa’adin tashin da kwamitin ta bayar, kana kuma su janye maganan kwashe kayansu cikin kwanaki biyu. ko azo masu ta hanyar da bazai masu dadi ba.
Shugaban kwamitin rage chunkoson kuwa, da aka tuntube shi ta wayar tarho, Kwamodo Tijjani Baba Gamawa ritaya, yace wan nan doka an basu ita kusan wata hudu da suka shige, amma sukayi kunnen Uwar shegu da batun, wan nan doka ce ta Gwamnati Jihar suma a matsayinsu na kwamiti basu isa su chanza ba.
Kana yace tunda an basu wa’adin tun farko, Kuma an basu filin da zasu baje kolinsu, a gwamnatance bamu ga dalilin da zasu ce ba’ayi masu adalci badata yanashi-yanashi ya bar gefen Kasuwar central market, kafin awa arba’in da takwas 48, wanda yaki ji baya ki gani ba.
Daga Adamu Shehu Bauchi
