Akwai Lauje Cikin Nadi A Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Wa Kyari – Matasan Arewa

An bayyana cewar ko shakka babu da akwai lauje cikin nadi a cikin tuhume-tuhumen da ake yi wa jajirtaccen Dan sanda Abba Kyari na karbar cin Hanci da rashawa daga hannun wani ?an damfara.

Shugaban kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu ne ya bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna dangane da wannan cece kuce da ake yi.

Gujungu ya ?ara da cewar ga duk wani ?an Najeriya mai kishin kasa ya yarda kuma ya sani cewar DCP Abba Kyari ?an sanda ne abin alfahari wanda ya tsayu wajen ganin al’amurra sun daidaita a ?asa, ta hanyar sanya kafar wando guda da duk wani tsagera a fadin Najeriya.

“Kyari ya bayar da gagarumar gudummawa wadda kowa ya yaba da ita wajen fasa garken bata gari musamman na sashin kudancin kasar nan, wanda hakan ya sa suka kullace shi har abin da ya faru yanzu ya faru.

Shugaban Matasan ya kara da cewar kasancewar yanzu an kafa kwamiti domin gudanar da bincike suna yi wa Kwamitin fatan Alkhairi da fatan yin aiki tsakani da Allah.

Dangane da batun shugabannin tsagerun kungiyoyin Inyamurai da Yarbawa wato Kanu da Igboho wadanda suke tsare a yanzu, Shugaban matasan arewa ya bukaci Shugaban ?asa ya tsayu sosai ya tabbatar a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Related posts

Leave a Comment