A?alla an ?one manyan motocin ?aukar kaya na Dangote Cement 11, a ranar Talata, yayin da hasalallun matasan Yarabawa su ka banka masu wuta.
An ?one motocin ne yayin da su ke ajiye a ?ofar shiga Masana’antar Dangote Cement, a garin Ibese, ?aramar Hukumar Yewa ta Arewa, Jihar Ogun.
Rikicin ya samo asali ne daga tankiya tsakanin ‘yan aca?a, wa?anda akasarin su Hausawa ne ‘yan Arewa, da kuma jami’an kar?ar ku?a?en harajin ta hanyar sayar da tikiti ga ‘yan aca?a.
Rigima ta fara kaurewa yayin da aka ?ara ku?in tikiti daga naira 600 zuwa naira 800.
Wa?anda fa?an ya yi muni a gaban su, sun tabbatar da cewa rikicin ya riki?e zuwa tantagaryar rikicin ?abilanci tsakanin Yarabawa da Hausawa, a daidai kusa da masana’antar siminti ta Dangote Cement da ke Ibesi.
Ganau ya tabbatar da cewa zuwa ranar Talata dai an tabbatar da kisan mutum bakwai.
Lokacin da wakilin Premium Times ya je wurin da aka yi rikicin a ranar Laraba, ya ga ?onannun motocin Dangote Cement guda bakwai a ?one ?urmus.
Wani mazaunin wurin mai suna Hamzat Ibrahim, ya shaida masa cewa an fara rikicin tun a ranar Litinin a kan farashin sayar da tikitin kar?ar haraji a hannun ‘yan aca?a masu haya da babura.
‘Hausawa sun doki mai sayar da tikiti. Su kuma matasan yankin su ka ri?a ?one kayayyakin Hausawa, har su ka kai ga ?one motocin Dangote.
?an Majalisar Jihar Ogun mai wakiltar Yewa ta Arewa 1, ya ce laifin gwamnati ne da kuma laifin kamfanin Dangote.
“Ta yaya za a ce kamfanin ?angote ba shi da garejin da za a ri?a ajiye motocin sa. Da su na can a ?e?ance da ba a je an yi masu ta’adi ba. Saboda haka ya kamata Gwamna da Dangote su zauna su samar da wurin ajiye motocin kamfanin sa da gaggawa.”
Daga nan sai ya yi kira da a ?ir?iro sarautar gargajiya a garin, ta yadda shugabanni gargajiya su ri?a sasanta ?ananan matsalolin cikin jama’a, kafin a yi sakacin da zai kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Kakakin ‘Yan Sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar wa wakilin mu faruwar lamarin, amma bai bayyana adadin yawan mutanen da su ka rasa rayukan su ba.
