Iran ta nuna matukar bacin ranta a kan wani hoton barkwanci da ya yi kama da shugaban juyin-juya-hali na kasar, Ayatollah Ruhollah Khomeini wanda aka wallafa a wata jaridar Saudiyya.
An sa hoton ne a wani rahoto da aka wallafa ranar Lahadi a jaridar ‘Al-Riyadh’, wadda ta danganta Iran da kashe-kashe.
A rahoton an sanya zanen hoton barkwancin na wani mutum da fuskarsa ta yi kama da ta Ayatollah Khomeini, amma kuma da yanayi na Shaidan.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana hoton a matsayin cin mutunci.
A baya-bayan nan Iran da Saudiyya sun dukufa wajen farfado da huldar diflomasiyya a takaninsu, wadda ta tabarbare a 2016 lokacin da masu zanga-zanga ‘yan Iran suka kutsa ofishin jakadancin Saudiyya a Tehran.
