Wasanni: Messi Ya Zama Dan Wasa Mafi Tsada A Duniya

Bayan komawar Lionel Messi taka leda a kungiyar kwallon Paris Saint-Germain, zai rika amsan N546m a mako kuma shine dan kwallo mafi yawan albashi a duniya.

GiveMeSport ta lissafo manyan yan kwallon duniya 10 da suka fi daukan albashi a fa?in duniya.

Dan wasan kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo na daukan £900,000 yayinda Neymar na kungiyar PSG na daukan £606,000.

Ga jerin yan kwallo 10 mafi yawan albashi a duniya, a cewar The Radio Times:

1- Robert Lewandowski – £350,000-a-mako(kimanin N200million) 2- David De Gea – £375,000-a-mako(kimanin N214million). 3. Kevin De Bruyne – £385,000-a-mako (kimanin N219million) 4. Kylian Mbappe – £410,000-a-mako (kimanin N233million) 5- Gareth Bale – £500,000-a-mako (kimanin N285million) 6. Luis Suarez – £575,000-a-mako (kimanin N327million) 7. Antoine Griezmann – £575,000-a-mako (kimanin N327million) 8- Neymar – £606,000-a-mako (kimanin N345million) 9. Cristiano Ronaldo – £900,000–a-mako (kimanin N512million). 10. Lionel Messi – £960,000–a-mako (kimanin N546million)

Related posts

Leave a Comment