Matsalar Tsaro Ta Kusan Zama Tarihi A Najeriya

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce matsalar tsaron da kasar ke fama da ita na daf da zama tarihi.

Yana magana ne lokacin da ya karbi bakuncin wani mai rike da sarautar gargajiya, wato Oluyin na Ekiti a Abuja, inda ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dokoki ta amince da kwarya kwaryar kasafin daya mika mata na kusan dala biyan 900, domin zuba su a harkar tsaron kasar.

Sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban ?asar Laolo Akande ya fitar, ta ambato yana cewa tuni shugaban ya kafa wani kwamiti da zai duba bukatun dukkanin hukumomin tsaron Najeriya domin a biya musu, ta yadda za a murkushe matsalar cikin gaggawa.

Tuni majalisar ta amince da bu?atar kashe kudaden.

Related posts

Leave a Comment